Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Faransa Ya Tsallake Rijiya Da Baya - 2002-07-15


'Yan sandan Faransa sun ce mutumin nan da yayi harbi da bindiga a lokacin faretin ranar samun 'yanci jiya lahadi a birnin paris, daidai lokacin da shugaba Jacques Chirac yake wucewa ta gabansa a cikin wata budaddiyar mota, ya furta cewa yayi niyyar kashe shugaban ne.

'Yan sanda sun ce wannan dan bindiga sunansa Maxime Brunerie mai shekaru 25 da haihuwa. Suka ce dan kungiyoyin banga ne masu ra'ayin 'yan Nazi. Wani gidan telebijin na kasa a Faransa ya ce mutumin ya jima yana fuskantar matsalolin tabuwar hankali.

Wannan lamari ya faru a kusa da wani dandalin da ake kira Arc de Triumphe, wanda aka gina domin karrama nasarorin soja da Faransa ta samu, inda Mr. Chirac yake duba sojoji masu fareti.

Shaidu sun ce wannan dan bindiga yana tsaye a cikin 'yan kallo sai ya zaro wata doguwar bindiga daga kwalin goge irin na turawa, ya kuma harba ta sau daya kafin a danne shi a kasa a daure shi.

Babu wanda ya ji rauni a wannan lamarin da jami'an Faransa suka ce kokari ne na kashe shugaban kasar.

Duk da wannan lamarin, an ci gaba da bukukuwa masu kayatarwa na ranar 'yancin kan kasa.

XS
SM
MD
LG