Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yanke Hukumcin Kisa Kan Sheikh Omar - 2002-07-15


Wata kotun kasar Pakistan ta samu masu kishin addinin Islama hudu da laifin sacewa da kashe wani dan jaridar Amurka, Daniel Pearl.

An yanke hukumcin kisa a kan babban wanda aka tuhuma, Ahmed Omar Sheikh, wanda aka haifa ya kuma yi karatu a kasar Britaniya. Mutane uku da aka ce ya hada baki da su kuma, dukkansu 'yan kasar Pakistan, zasu shafe tsawon rayuwarsu a kurkuku.

Ana zartas da hukumcin kisa a Pakistan ta hanyar ratayewa. Lauyoyin kariya sun ce zasu daukaka kara.

Mr. Pearl ya bace ranar 23 ga watan Janairu a birnin Karachi dake kudancin Pakistan, inda yake neman labarai game da masu kishin addinin Islama. Wani faifan bidiyo mai munin gani da aka samo daga baya, ya nuna cewa an kashe shi.

An tuhumi Sheikh Omar da laifin kafa tarkon kama wannan dan jarida ta hanyar yi masa karyar cewa yana shirya masa yin hira da wani mai kishin addini.

'Yan sanda sun yi imanin cewa gawar Mr. Pearl suka gano a cikin wani rami a birnin Karachi cikin watan Mayu, amma har yanzu ba a tabbatar da hakan ba.

XS
SM
MD
LG