Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwayar Cutar Zazzabin Cizon Sauro Dadaddiya Ce A Duniya - 2002-07-18


An gano cewar kwayar halittar cutar nan mai haddasa zazzabin cizon sauro, dadaddiyar halitta ce kuma mai fannoni da yawan gaske, abinda zai sa a kara samun wahala wajen kirkiro da allurar rigakafin kamuwa da cutar. Wannan bayani, shine sakamakon binciken da masana a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Amurka suka gudanar, a bayan da suka nazarci tsarin halittar kwayar cutar.

Wakiliyar Muryar Amurka, Jessica Berman, ta ce a da can, maganin nan mai suna "Chloroquine" yana da kaifi sosai wajen warkar da cutar maleriya, watau zazzabin cizon sauro. Amma a karshen shekarun 1950, sai aka fara ganin cutar tana jurewa maganin Chloroquine a nahiyar kudancin Amurka da kuma yankin kudu maso gabashin Asiya.

Kwararru sun dauka cewar daga wadannan yankuna biyu ne nau'o'in kwayar cutar maleriya masu jurewa maganin Chloroquine suka yadu zuwa sauran sassan duniya. Amma kuma sabbin alkaluman da masana a Cibiyar Nazarin Cututtuka Masu Yaduwa ta Amurka suka buga cikin mujallar "Nature" sun nuna cewa kwayar cutar ta Maleriya ta fara jurewa maganin Chloroquine a yankuna dabam-dabam har guda hudu a lokaci guda.

Akwai yankuna guda biyu a nahiyar Amurka ta Kudu, da yanki guda a Papua New Guinea da kuma guda a kudu maso gabashin nahiyar Asiya.

Masu bincike sun kai ga cimma wannan shawara, a bayan da suka nazarci tsarin jigidar halittar kwayoyin cutar maleriya dabam-dabam har guda 87 da aka kwaso daga kowane lungu na duniya. Xin-Zhuan Su (Sin-Schwan-Soo), shine babban marubucin rahoton, ya kuma ce...

"...Wannan bincike ya nuna cewa kwayar cutar Maleriya tana da sarkakiya, tana kuma da nau'o'i masu yawa. Sannan mun gano cewa yawan jurewa maganin Chloroquine ya zarce yadda muka yi tsammani tun da farko. Wannan yana nuna cewar lallai ya kamata mu sanya idanu sosai a kan yadda ake amfani da maganin na Chloroquine, mu kuma kafa wani shirin na sa idanu idan muka gabatar da sabbin magunguna na warkar da cutar."

A wani rahoton na biyu, wanda shi ma aka buga cikin mujallar "Nature", ayarin masu binciken na Mr. Xin-Zhuan, sun gano, a bayan da suka nazarci kwayoyin halitta fiye da 200, cewar kwayar cutar maleriya ta kai shekara dubu 100 zuwa dubu 180 a duniya. Ayyukan nazarce-nazarce marasa zurfi da aka yi a can baya, sun ce kwayar cutar ba ta shige shekaru dubu 3 zuwa dubu 5 da bulla a duniya ba. Masanan sun iya gano yawan shekarun kwayar cutar ne ta hanyar irin bambance-bambancen dake cikin kwayoyin halittarta, watau bambance-bambancen kwayoyin halitta irin wadanda ke wakana cikin wani tsawon lokaci.

Mr. Xin-Zhuan ya ce wannan sarkakiya ta kwayoyin halittar kwayar cutar, tana nufin cewa za a fuskanci kalubala wajen kirkiro da maganin yin rigakafin kamuwa da cutar maleriya ko zazzabin cizon sauro.

Jami'in ya ce, "An shafe shekaru 15 zuwa 20 ana gudanar da ayyukan binciko maganin yin rigakafin kamuwa da zazzabin cizon sauro. Amma har yanzu ba mu da wani abu da yayi kama da maganin rigakafi. Wannan lamari yayi daidai da abinda muka gano, cewar kwayar cutar maleriya tana da kwayoyin halitta masu sarkakiya, kuma tana da saurin canja nau'i, ta yadda zata iya takalar duk wani maganin da aka zuba mata...."

Wannan kuwa, mummunan labari ne ga mutane kimanin miliyan 300 a fadin duniya wadanda suke kamuwa da kwayar cutar maleriya ko zazzabin cizon sauro a kowace shekara, da kuma mutane miliyan biyu, akasarinsu yara matasa da jarirai wadanda suke mutuwa kowace shekara a sanadin zazzabin maleriya.

XS
SM
MD
LG