A Nijeriya, makeken kamfanin man ferur na Amurka mai suna ChevronTexaco ya cimma yarjejeniya da mata masu zanga-zanga, domin akwo karshen kofar ragon da wadannan mata suka yi wa daya daga cikin manyan dandalolin jigilar mai zuwa kasashen waje na wannan kamfani.
Matan, wadanda ba su dauke da makami sun kama mutane suka yi garkuwa da su, suka kuma hana aiki na tsawon kwanaki goma a dandalin jigilar mai na Escravos, inda suka bukaci a ba su ayyukan yi a kuma gudanar da ayyukan raya kasa a yankunansu.
Kamfanin ChevronTexaco ya fada jiya laraba cewar zai ringa samar da ayyukan yi a kai a kai ga mutanen yankin, zai kuma samar da kudin gudanar da ayyukan samar da kayayyakin bukatu.
A daidai lokacin da ake kawo karshen wannan cirko-cirko jiya laraba ne kuma, sai ga labarin cewa wasu matan dabam kuma sun kama tasoshi akalla guda hudu na famfon man fetur na kamfanin ChevronTexaco. Wadannan tasoshi ne ke tura mai zuwa dandalin Escravos, daga inda ake jigilarsa zuwa kasashen waje.
Babu wani labari kan tattaunawar da ake shirin fara yi tsakanin kamfanin da wannan kungiya ta biyu ta mata.
Koda yake Nijeriya tana daya daga cikin kasashen da suka fi arzikin man fetur a duniya, kusan rabin al'ummar kasar suna zaune cikin matsanancin talauci. Kama wuraren hako mai ya zamo ruwan dare. Amma akasari mazaje ne dauke da makamai suke aikata wannan, ba mata ba.