Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Zambiya Ya Kare Matakan Da Ake Dauka Na Gurfanar Da Mutumin Da Ya Gada A Gaban Shari'a - 2002-07-18


Shugaba Levy Mwanawasa na Zambiya ya bayyana kokarin da ake yi an bincike tare da gurfanar da mutumin da ya gada, Frederick Chiluba, a gaban kotu, da cewa ba na neman cin zarafi ba ne.

Cikin hirar da aka yi da shi a wani shirin gidan telebijin na Muryar Amurka mai suna "Straight Talk Africa" jiya laraba, shugaban ya kare matakin da ya dauka na kawar da kariyar da Mr. Chiluba yake da ita ta gurfana gaban shari'a. Har ila yau shugaban na Zambiya ya ce a karkashin tsarin mulkin kasarsa, ba a daukar Mr. Chiluba a zaman wanda yayi laifi, har sai kotu ta same shi da laifi.

Tun fari a jiya larabar, tsohon shugaban ya samu nasara a gaban kotu, a lokacin da babbar kotun kasar ta hanawa gwamnati ci gaba da binciken Mr. Chiluba na wani lokaci. A cikin hukumcin da ta yanke, alkali Anthony Nyangulu ya ce tilas sai kotu ta nazarci matakan da majalisar dokoki ta dauka na janye kariyar Mr. Chiluba kafin a fara duk wani bincike kansa.

A ranar talata ba tare da wata hamayya ba, majalisar dokokin kasar Zambiya ta jefa kuri'ar dage kariyar Mr. Chiluba domin ya fuskanci zargin zarmiya. Shugaba Mwanawasa ya nemi majalisar da ta cire kariyar ne, yana mai zargin cewa tsohon shugaban ya sace miliyoyin daloli daga baitulmalin gwamnati a lokacin da yake shugabanci. Mr. Chiluba ya musanta zargin.

XS
SM
MD
LG