Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shayar Da Jarirai Nono Yana Rage Wa Uwa Kasadar Kamuwa Da Cutar Sankara - 2002-07-19


Likitoci masu bincike sun ce wani nazarin da aka gudanar a kasashe masu yawa a duniya ya gano cewar uwayen dake da 'ya'ya da yawa, suke kuma shayar da jariransu nonon uwa, suna rage kasadarsu ta kamuwa da cutar sankara.

Wannan nazarin da aka bayyana sakamakonsa cikin mujallar kiwon lafiya ta Britaniya mai suna "Lancet" ya kunshi mata dubu 150 a kasashe 30 masu arzikin masana'antu.

Nazarin ya gano cewar a takaice, matan dake kamuwa da cutar sankarar nono, ba su da 'ya'ya masu yawan wadanda ba su da wannan cuta.

Haka kuma nazarin ya gano cewar kashi 29 daga cikin 100 na matan da ba su taba bada jariransu nono ba sun kamu da cutar sankara ta nono, yayin da kashi 21 daga cikin 100 na matan da suka shayar da 'ya'yansu ne kawai suka kamu da cutar.

Hukumar lafiya ta duniya, ta shawarci uwaye mata da su shayar da 'ya'yansu nonon uwa na tsawon shekaru biyu.

XS
SM
MD
LG