Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Iraniyawa Da Su Fito Domin Zanga-Zangar Nuna Kin Jinin Amurka - 2002-07-19


Kungiyoyin Musulmi da kuma gwamnatin Iran sun bukaci dukkan Iraniyawa da su shiga cikin zanga-zangar ad za a yi yau jumma'a a duk fadin kasar da nufin nuna kin jinin take-taken Amurka.

Shi ma Ayatollah Jalaledin Taheri yana goyon bayan wannan zanga-zanga. Shi ne babban limamin nan da yayi murabus a makon da ya shige a birnin Isfahan, a bayan da ya soki shaihunan malamai masu ra'ayin 'yan mazan jiya dake kawo cikas ga kokarin yin sauye-sauye a kasar.

Amma kuma a jiya alhamis, kamfanin dillancin labaran Iran, ya ambaci Ayatollah Taheri yana fadin cewa Iraniyawa ba su kyale baki suna yi musu katsalanda cikin harkokinsu.

Wannan kuwa shagube ne ga kalamun shugaba Bush na Amurka, wanda a makon jiya ya ce ya kamata shugabannin Iran su saurari bukatun al'ummarsu na neman karin 'yancin walwala da na siyasa.

Jim kadan a bayan wannan furuci na Mr. Bush, shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khameini, ya ja kunnen 'yan Iran game da sakamakon kalubalantar tsarin mulkin kasar, ya kuma bukaci da a yi wannan zanga-zanga na nuna kin jinin take-taken Amurka.

XS
SM
MD
LG