Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Harkokin Wajen Larabawa Sun Samu Karin Guiwa Bayan Tattaunawa Da Shugaba Bush - 2002-07-19


Ministocin harkokin wajen wasu kasashe uku na larabawa sun ce sun samu kwarin guiwa, a bayan tattaunawar da suka yi a fadar White House da shugaba Bush kan yiwuwar kirkiro da kasar Falasdinu.

Ministocin harkokin waje Marwan al-Muasher na Jordan, da Ahmed Maher na Masar da kuma Sa'ud al-Faisal na Sa'udiyya, sun gana da shugaban na Amurka jiya alhamis a fadar White House.

Ministan harkokin wajen Misra, Ahmed Maher, ya ce dukkansu suna kwadayin ganin kasar Falasdinu zaune cikin lumana da kwanciyar hankali a gefen kasar Isra'ila.

Ya ce irin rawar da shugaban Falasdinawa Yasser Arafat zai taka ba ta cikin tattaunawar ranar alhamis, im ban da dacewar ra'ayin cewar al'ummar Falasdinu ne kawai suke da ikon zaben shugabanninsu.

Tun da fari, ministocin sun bai wa jami'an Amurka wani shirin yin sauyin siyasa a tsarin gudanar da mulkin Falasdinawa. An ce rahoton ya tanadi kafa sabon tsarin mulki rubutacce na Falasdinawa, da zababbiyar majalisar dokoki da kuma mukamin firayim minista.

Shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, zai rike mukamin shugaban kasa, wanda za a zabtare masa iko.

XS
SM
MD
LG