Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Da 'Yan Tawayen Sudan Sun Daidaita Kan Muhimman Batutuwa - 2002-07-21


Gwamnatin Sudan da 'yan tawayen kudancin kasar sun cimma daidaituwa a kan wasu muhimman batutuwa da zasu kai ga cimma kammalalliyar yarjejeniya ta zaman lafiya domin kawo karshen yakin basasar shekaru 19.

A bayan da suka yi makonni suna tattaunawa a garin Machakos na kasar Kenya, wakilai na gwamnatin Sudan da kuma na kungiyar 'yan tawayen SPLA sun ce sun warware batutuwa biyu da suka dade suna hana ruwa gudu: batun cire addini a harkokin mulkin kasa, da kuma bai wa jama'a ikon zabin cin gashin kai.

Mai bai wa shugaban Sudan shawara kan ayyukan zaman lafiya, Ghazi Salah al-Din, da kakakin 'yan tawaye, Samson Kwaje, duk sun fada jiya asabar a birnin Nairobi cewa suna sa ran warware sauran batutuwan da suka rage cikin sauki idan sun sake ganawa cikin wata mai zuwa a babban birnin na Kenya.

Suka ce zagaye na gaba na tattaunawar da za a yi zai mayar da hankali kan rarraba ikon mulki, da raba arzikin man kasar da kare hakkin bil Adama da kuma tsagaita wuta.

Shugaba Daniel Arap Moi na kasar Kenya, shine ya dauki nauyin gudanar da wannan tattaunawa da aka fara yi ranar 17 ga watan Yuni karkashin inuwar Kungiyar Raya Kasa ta Gwamnatocin kasashen yankin.

XS
SM
MD
LG