Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Morocco Da Spain Sun Warware Rikici Kan Tsibiri - 2002-07-21


Morocco da Spain sun warware rikicin soja da na diflomasiyyar da suke yi a game da wani dan karamin tsibiri a tekun bahar Rum, har ma kasar Spain ko Andalus ta janye dukkan sojojinta daga can.

Hukumomin Spain sun fada asabar din nan cewa kasashen biyu sun yarda wannan tsibiri zai koma yadda yake kafin abubuwan da suka faru cikin wannan watan. Spain ta godewa sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell saboda shiga tsakanin da yayi.

Dukkan kasashen biyu suna ikirarin mallakar wannan tsibirin da Morocco take kira Leila, yayin da Spain take kiransa Perejil.

A farkon watan nan Morocco ta tura sojoji guda 12 zuwa kan tsibirin domin magance abinda ta kira ayyukan safarar miyagun kwayoyin da ake yi daga can.

Kwanaki a bayan wannan, an tura sojojin Spain wadanda a cikin lumana suka tasa keyar sojojin Morocco daga wannan tsibirin da babu wanda ke zama a kansa.

XS
SM
MD
LG