Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Uganda Suna Farautar Direban Tankar Man Fetur - 2002-07-21


Jami'an tsaro a kasar Uganda suna farautar direban wata tankar daukar mai, wanda motarsa ta kara da wata motar safa a ranar alhamis ta kama da wuta, sannan ta kashe mutane su akalla 60.

Wani kakakin hukumar tsaron kasar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AP cewar 'yan sanda sun kama makanikin wannan motar daukar mai, sannan suna neman direban, wanda aka yi imanin ya tsere jim kadan kafin motar tayi bindiga.

Kakakin ya ce makanikin ya shaida musu cewar burkin motar tasu ce ta ki yin aiki lokacin ad suke gangarowa daga kan wani tudu kusa da garin Rutoto dake yamma da Kampala, babban birnin kasar.

Motar ta kwace daga hannun direban ta kara da wannan motar safa, abinda ya haddasa bindiga tare da wutar da ta baibaye motar safar baki dayanta.

An gano gawarwaki guda 59 da suka kone kurmus. Hukumomin Uganda suka ce wadanda suka mutu sun hada da 'yan Uganda su 38 da kuma wasu mutane 18 'yan kasar Kwango.

XS
SM
MD
LG