Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Jami'an Isra'ila Da Na Falasdinawa Sun Tattauna - 2002-07-21


Jami'an Isra'ila sun ce a shirye kasarsu take ta kara daukar matakan biyan bukatun Falasdinawa a yankin Yammacin kogin Jordan da zirin Gaza.

Suka ce ministan harkokin wajen Isra'ila, Shimon Peres, da babban jami'in shawarwari na Falasdinawa, saeb Erekat, sun tattauna hanyoyin kyautata halin da ake ciki a yankunan Falasdinawa a lokacin da suka tattauna jiya asabar.

Ba a bada karin bayani kan wannan tattaunawa tasu ba, amma sassan biyu sun shirya sake ganawa cikin 'yan kwanakin dake tafe.

Tun a ranar laraba aka shirya gudanar da tattaunawar ta jiya asabar, amma sau biyu Isra'ila tana dagewa a bayan hare-hare biyu da suka kashe mutanw 12 tare da 'yan kunar bakin wake su biyu.

XS
SM
MD
LG