Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Chevron Texaco Ya Dakatar Da Tono Mai Cikin Teku A Nijeriya Saboda Gobara - 2002-07-22


Makeken kamfanin man fetur na Amurka mai suna Chevron-Texaco ya ce ya dakatar da tono mai daga cikin teku a kusa da gabar Nijeriya, bayan da wuta ta barke ranar asabar a dandalin da kamfanin ke amfani da shi wajen jigilar mai zuwa kasashen waje.

Kamfanin ya ce wannan matakin da ya dauka zai hana shi tono ganga dubu 300 na mai a kowace rana. Ya ce tuni har wannan gobara ta sa an yi hasarar ganga dubu 100 na danyen mai.

Wani kakakin kamfanin ya ce dakatar da tono man mataki ne kawai na yin rigakafi, kuma tuni an samu nasarar rutsa wannan wuta a wuri guda.

Gobara ta tashi ranar asabar a lokacin da tsawa ta fadi kan daya daga cikin tankokin ajiye mai a wannan makeken dandali. A wannan dandalin ne wasu daruruwan mata suka yi zanga-zangar kwanaki goma, suka gurgunta ayyukan tonowa da jigilar man fetur.

XS
SM
MD
LG