Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Ja Da Baya Daga Barazanar Korar Iyalan Mahara - 2002-07-22


Isra'ila ta fara janye barazanar da take yi ta mayar da iyalan Falasdinawa 'yan kai harin kunar-bakin wake na yankin Yammacin kogin Jordan zuwa zirin Gaza.

Ministan shari'ar Isra'ila, Meir Sheetreet, ya ce, za a bi diddigin kowane Bafalasdine dan kunar bakin wake, domin a takaita batun korar zuwa zirin Gazar kawai, ga dangin da suke da masaniya gameda irin wannan farmaki, amma kuma su ka ki kai rahoto domin a hana kaddamar da shi.

Amma kungiyar Falasdinawa mayakan sa-kai ta dakarun shahada na al-Aqsa ta ce, za ta darfafi iyalan jami'an Isra'ila, muddin aka mayar da wani dan harin kunar bakin wake zirin na Gaza.

Wannan barazana da Firayim ministan Isra'ila, Ariel Sharon, ya ke yi, ta iza keyar irin wadannan Falasdinawa su fice daga yankin Yammacin kogin Jordan, ta gamu da suka mai gauni daga nan Amurka, da kungiyar kasashen turai, da kuma kasashen Larabawa.

XS
SM
MD
LG