Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Sadarwa Na WorldCom Ya Ce Ya Talauce, Yana Neman Kariya Daga Kotu - 2002-07-22


Makeken kamfanin sadarwa na WorldCom, ya nemi kotu da ta shiga tsakaninsa da masu binsa bashi, a kariyar talauci mafi girma da wani kamfani ya taba nema a tarihin Amurka.

Wannan matakin ya zo kusan wata guda cur a bayan da kamfanin ya ce yayi amfani da wata dabarar yin rufa ido, domin boye sawun wasu kudade kusan dala miliyan dubu hudu da ya kashe.

Shugaban kamfanin WorldCom, John Sidgmore, ya fada ranar lahadi cewar kamfaninsa yana neman kariya daga masu binsa bashi a karkashin dokokin shiga cikin talauci na Amurka, matakin ad zai bai wa kamfanin damar sake garambawul ga tsare-tsarensa na kudi yayin ad zai ci gaba da aikinsa.

Mr. Sidgmore ya ce ba a sanya rassan kamfanin dake wasu kasashe cikin wannan takarda ta neman kariya ba.

WorldCom shine kamfanin tarho na biyu wajen girma a fadin Amurka, kuma shine ke rike da hanyoyin sadarwar duniyar gizo, watau Internet, mafi girma a duk duniya.

Jami'an kamfanin suka ce suna sa ran zasu ci gaba da samar da layukan tarho da na duniyar gizo ba tare da katsewa ba ga mutane miliyan 20 masu hulda da kamfanin.

XS
SM
MD
LG