Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Nuna Karin Alamun Rashin Jin Dadin Take-Taken Isra'ila - 2002-07-25


Jiya laraba Amurka ta kara nuna alamun rashin jin dadinta da wani harin da Isra'ila ta kai a zirin Gaza ranar litinin, ta yin amfani da jirgin saman F-16 kirar Amurka, inda ta kashe fararen hula masu yawa a cikin wata unguwa.

Wakilin Muryar Amurka, David Gollust, ya ce jami'an gwamnatin Amurka sun nuna cewar ba za a zauna a zahiri a rubuta takardar zargin Isra'ila da cewar yin amfani da makamai kirar Amurka da tayi a zirin Gaza ya sabawa dokokin sayar da makamai na Amurka ba. Amma kuma, ma'aikatar harkokin waje a nan Washington ta gargadi Isra'ila cewar an sa idanu sosai kan irin take-takenta, ta kuma yi kashedin cewa idan Isra'ila ta kuskura tayi amfani da makaman da Amurka ta sayar mata ta hanyoyin da ba su dace ba, to zata dandana kudarta.

Wata dokar da aka kafa a shekarar 1976 ta haramta yin amfani da makaman Amurka da aka sayarwa da kasashen waje, sai fa idan a zahiri wajen kare kai ne, ko kuma tabbatar da tsaron cikin gida. An bukaci ma'aikatar harkokin waje da ta sanar da majalisar dokoki idan har ta tabbatar da cewa an keta ka'idojin sayar da makaman sosai.

A lokacin da yake magana da 'yan jarida, kakakin ma'aikatar harkokin waje, Richard Boucher, ya ce babu wani rahoton da aka aikewa da majalisar dokoki dangane da harin na Gaza. Amma duk da haka, ya ce Amurka ta damu ainun da irin take-taken Isra'ila wajen kai wannan harin, harin da fadar shugaban Amurka ta White House ta bayyana a zaman na nuna isa kawai.

Mr. Boucher ya ce, "...ba mu rubuta wani rahoto irin wannan ba tun lokacin da aka fara tashin hankali na baya-bayan nan a Gabas ta Tsakiya. Amma kuma, mun bayyana a fili cewar mun damu sosai da wasu daga cikin dabarun da Isra'ila take aiki da su, da kuma take-takenta, ciki har da farautar wasu mutane domin ta kashe su, da matakai irin wannan masu jefa fararen hula cikin hadari. A saboda haka muna ci gaba da sa idanu sosai kan matakan da Isra'ila take dauka. Muna kira ga Isra'ila da tayi tunanin sakamakon daukar matakai irin wadannan."

A wannan hari na zirin Gaza, an yi amfani da jirgin sama kirar F-16 wanda Amurka ta bayarwa da Isra'ila, wajen jefa wani bam mai nauyin ton guda wanda ya ragargaza jerin gidajen kwana cikin wata unguwa, ya mayar da su kango, ya kuma lalata wasu dake kusa. An kashe shugaban bangaren soja na Hamas, Malam Shehade, tare da wasu Falasdinawa fararen hula su 14, cikinsu har da yara kanana guda 9.

Kakakin ma'aikatar harkokin waje, Richard Boucher, ya ce Amurka zata shiga cikin muhawarar da Kwamitin sulhun MDD zai yi kan harin na Gaza, sai dai kuma wani babban jami'i ya ce watakila Amurka zata yi adawa da kudurin yin tur da Isra'ila wanda kasashen larabawan suka zana idan har an zo jefa kuri'a a kai. Sa'udiyya da wasu kasashen larabawan ne suka nemi da a yi wannan muhawara.

Mr. Boucher ya ce gwamnatin shugaba Bush tana ci gaba da mayar da hankalinta a kan hanyoyin farfado da shirin samar da zaman lafiya a yankin ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen sauyi ga tsarin siyasa da na tsaron Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG