Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Caccaki Isra'ila A Majalisar Dinkin Duniya... - 2002-07-25


Jakadan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya ce kazamin harin nan ta sama, da Isra'ila ta kai a birnin Gaza, wani babban laifin yaki ne, wanda ya kamata sabuwar kotun duniya kan aikata laifuffukan yaki ta takala.

Jakada Nasser al-Kidwa ya yi wannan korafi ne, a daidai lokacin da Kwamitin Sulhun MDD yake yin muhawara, game da wannan farmaki na ranar litinin, kamar yadda jami'an diflomasiyyar kasashen Larabawa a majalisar suka bukata.

Yanzu haka dai, wani jakadan Isra'ila a majalisar, ya bayyana juyayi sosai game da wannan hari. Amma kuma, ana kyautata zaton kwamitin sulhun zai jinkirta daukar wani mataki gameda kudurin da kasashen Larabawan suka gabatar, wanda yake yin Allah wadai da wannan raraka da Isra'ila ta kai, tare da jadadda bukatar janye dakarun Isra'ilar daga biranen Falasdinawa da suka mamaye.

Wannan hari na ranar litinin a birnin Gaza, ya yi sanadiyyar kashe wasu Falasdinawa farar hula su 14, ciki har da wanda aka auna harin kansa, wani jagoran Musulmi mayakan sa kai na kungiyar Hamas.

Yanzu haka dai, Hamas ta lashi takobin cewa, sai jini ya kwarara, idan ta zo daukar fansa.

A halin da ake ciki kuma, ofishin jakadancin Amurka dake Isra'ila yana yin gargadi ga Amurkawa, da su yi taka tsan-tsan, saboda yiwuwar fuskantar farmaki daga mayakan sa kan kungiyar Hamas. Ofishin yayi kira ga dukkan Amurkawa dake Isra'ila da su rage kasadar jefa kansu cikin hatsari, su na yin kaffa-kaffa sosai, a lokutan da suke kai ziyara kowane yanki na Isra'ila.

Ofishin jakadancin ya ce, hususan, ya zama wajibi, ga Amurkawa su rika yin hattara a gidajen abinci, da kasuwanni, da sauran yankuna, wuraren da jama'a su kan taru.

XS
SM
MD
LG