Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Musanta Cewar Tana Matsawa Nijeriya Lambar Ta Fice Daga Kungiyar OPEC - 2002-07-26


Wani babban jami'in jakadancin Amurka ya kammala rangadin kwanaki biyar a kasashen Afirka uku masu arzikin man fetur, yayin da ake samun rahotannin cewa Amurka tana matsawa Nijeriya, kasar da ta fi kowacce arzikin man fetur a Afirka, lambar da ta fice daga cikin kungiyar OPEC.

Mataimakin sakataren harkokin waje mai kula da harkokin Afirka, Walter Kansteiner, ya kammala rangadin nasa jiya alhamis, inda ya gana da shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, a birnin Abuja. Tun fari ya ziyarci kasashen Angola da Gabon.

A bayan ganawar da yayi da shugaban na Nijeriya, Mr. Kansteiner ya ce yankin mashigin tekun Guinea da harkar tonon mai da ake yi a wurin, suna da matukar muhimmanci ga Amurka. Amma ya musanta rahotannin cewa Amurka tana matsawa Nijeriya lambar da ta fice daga cikin kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC.

Ya ce ba a tattauna wannan batu ba a lokacin tattaunawarsu da shugaba Obasanjo. Tun da fari, ministan yada labaran Nijeriya, Jerry Gana, ya ce Amurka ta matsawa Nijeriya lambar da ta bar kungiyar OPEC. Ya ce gwamnatin Nijeriyar tayi adawa da hakan.

Nijeriya tana daya daga cikin muhimman masu samar da man fetur ag Amurka. Masu fashin baki sun ce Nijeriya zata iya samar da mai da yawan gaske, mai dan karen arha idan ta bar kungiyar OPEC, abinda zai yi kyau sosai ya kuam zamo abin alheri ga Amurka.

XS
SM
MD
LG