Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Shiga Gaza Da Tankoki Da Motocin Rushe Gine-Gine - 2002-07-26


Wasu Falasdinawa wadanda su ka shaida abinda ya wakana, sun ce sojojin Isra'ila da tankokin yaki, gami da motocin rushe gine-gine, sun kutsa zuwa cikin zirin Gaza, suka dagargaza wasu gine-gine guda biyu, da kuma wani ofishin 'Yan sandan Falasdinawa.

Shaidun sun ce an jikkata akalla Falasdinawa biyu 'yan bindiga, a wani gumurzu da aka yi a kusa da birnin Gaza tunda jijjifin yau juma'a.

Har yanzu, rundunar sojjoin Isra'ila ba ta ce uffan ba a game da wannan farmaki.

Jiya a nan birnin Washington, Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya nuna damuwa game da yadda Isra'ila ta yi amfani da wasu jiragen yaki, kirar Amurka a wani hari da ta kaiwa birnin Gaza a farkon wannan makon, wanda ya yi sanadiyyar kashe wasu farar hula su 14.

Duk da haka, Mr. Powell bai nuna alamun cewa, mai yiwuwa Washington za ta dauki matakin ladabtar da gwamnatin Isra'ila ba.

XS
SM
MD
LG