Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Kudurin Kafa Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida - 2002-07-27


Majalisar wakilan Amurka ta jefa kuri'ar amincewa da kafa ma'aikatar tsaron cikin gida ta tarayya, inda wakilai 295 suka amince, wassu guda 132 kuma suka jefa kuri’ar rashin amincewa.

A yanzu, majalisar ta wakilai zata zauna domin daidaita wannan kuduri nata da wanda majalisar dattijai ta zartas kafin a turawa shugaba Bush.

Kudurin na majalisar wakilai ya tanadi tsame ma'aikatan wannan sabuwar ma'aikata daga wasu dokokin kwadago na tarayya. Mr. Bush yana son ita ma majalisar dattijai tayi hakan, har ma yayi barazanar cewa zai hau kujerar-na-ki idan ba a tanadi cire ma'aikatan wannan ma'aikata daga karkashin wasu dokokin kwadago na tarayya ba.

Shugaban ya ce tilas ne a bai wa sabuwar ma'aikatar sukunin dage ma'aikata daga wannan wuri zuwa wancan cikin gaggawa domin takalar duk wata barazanar da za a iya fuskanta a wani wuri, a kuma samu sukunin canja ma'aikatan da ba su aikinsu da kyau cikin gaggawa.

Sabuwar ma'aikatar zata kula da ayyukan wasu hukumomi 22 na tarayya, wadanda a hade suna da ma'aikata dubu 170.

XS
SM
MD
LG