Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Zata Gina Masana'antun Nukiliya Har Shida A Iran - 2002-07-27


Rasha ta bada sanarwar kulla sabuwar yarjejeniyar cinikayya da kasar Iran, wadda ta hada da gina sabbin masana'antun sarrafa makamashin nukiliya har guda shida.

Ana sa ran wannan matakin zai janyo adawa mai tsananin gaske daga fadar shugaban Amurka ta White House.

Jiya jumma'a a birnin Moscow jami'an Rasha suka bada cikakken bayanin wannan yarjejeniyar cinikayya. Za a gina hudu daga cikin wadannan masana'antun sarrafa makamashin nukiliya a Bushehr dake kudancin Iran, inda tuni aka fara gina wata masana'antar ta sarrafa nukiliya da ake cacar baki a kai. Za a gina wasu guda biyu a Ahvaz, dake kusa da nan.

Hukumomin Rasha sun dage, wajen jaddada cewar wadannan masana'antu na samar da makamashi ne kawai. Amma ita ma Amurka ta dage wajen jaddada yin adawarta da duk wani tallafin da Rasha take bayarwa a kokarin kafa masana'antar nukiliya a Iran.

Amurka ta ce Iran tana goyon bayan ayyukan ta'addanci, tana kuma tsoron cewa Iran zata yi amfani da fasahar Rasha wajen gina makaman nukiliya. Shugaba Bush ya bayyana Iran a zaman daya daga cikin kasashe ukun da ya ce mamugunta ne wadanda ke yin barazana ga tsaron lafiyar duniya.

XS
SM
MD
LG