Mutane akalla 78 fararen hula 'yan kallo sun mutu, wasu fiye da 100 suka ji rauni a lokacin da wani jirgin saman yaki ya fado a wani wurin bukin gwajin jiragen sama ranar asabar a yankin yammacin kasar Ukraine.
Yawan mutanen da suka mutu zai iya haurawa sama, yayin da jami'ai a birnin Lviv suka ce da yawa daga cikin wadanda suka ji rauni suna kwance rai hannun Allah.
Shaidu suka ce matuka biyu na wannan jirgin yaki samfurin Sukhoi SU-27 kirar Rasha, suna gwajin wasu dabarun juyawa da jirgin a sama ne a lokacin da ya kwace musu.
Matuka jirgin su biyu sun tsirgo kasa cikin laima ta musamman suka kubuta da rayukansu, amma sai jirgin ya fada a tsakiyar 'yan kallon da suka taru a wannan fili.
Shugaba Leonid Kuchma ya kori kwamandan mayakan saman kasar daga kan mukaminsa, ya kuma ce zai haramta dukkan bukukuwan gwajin jiragen sama a kasar.
An yi imanin cewa wannan shine hadari mafi muni da daukar rai cikin tarihi a wurin wasan nunin jiragen sama. Har yanzu ba a san musabbabin kwacewar jirgin daga hannun matukansa ba.