Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Powell Yana Rangadin Neman Cimma Zaman Lafiya Tsakanin Indiya Da Pakistan - 2002-07-28


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, zai gana yau lahadi da firayim minista Atal Behari Vapayee na Indiya, domin tattauna kawo karshen zaman tankiyar shekaru fiye da hamsin a tsakanin makwabtan biyu abokan gabar juna, kuma masu makaman nukiliya.

Jiya asabar ya gana da ministan harkokin wajen Indiya, Yashwant Sinha, wanda ya ce har yanzu pakistan ta kasa hana Musulmi 'yan aware tsallakawa zuwa cikin bangaren Indiya a yankin Kashmir.

Pakistan ta nace kan cewa ta dage a kokarin hana 'yan kishin Kashmir a nata bangaren suna tsallakawa cikin bangaren Indiya.

A bayan ganawar da zai yi da Mr. Vajpayee, Mr. Powell zai zarce zuwa birnin Islamabad domin ganawa da shugaban Pakistan, Pervez Musharraf.

Mr. Powell ya ce akwai bukata ga kasashen Indiya da Pakistan su fara tattaunawa da juna, ko kuma zasu fuskanci hadarin ci gaba da yin zaman tankiya. Amma kuma ya ce babu tabbas wannan kokari nasa zai haifar da ci gaba a kokarin sasanta sassan biyu.

XS
SM
MD
LG