Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nelson Mandela Yace Zai Yi Wa Mbeki Magana Kan Cutar Kanjamau Ta AIDS - 2002-07-28


Tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela, ya ce zai yi magana da mutumin da ya gaje shi, Thabo Mbeki, a kan ya samar da karin magungunan yakar cutar AIDS ga al'ummar kasar.

An sha sukar Mr. Mbeki a saboda kin tashi tsaye wajen yakar cutar a kasarsa, inda aka ce mutane miliyan 4 da dubu 700 aka tabbatar suna dauke da kwayar halittar cuta ta HIV mai janyo cutar AIDS.

Mr. mandela yayi alkawarin tayar da wannan batu idan ya gana da Mr. Mbeki, a bayan tattaunawar da yayi da Abdul-Razak "Zackie" Achmat dan rajin kare hakkin masu fama da cutar AIDS, wanda ya ki yarda ya sha maganin sassauto da cutar AIDS har sai gwamnati ta yarda ta samar da shi ga jama'ar kasar.

Kasar Afirka ta Kudu ta fi kowace kasa a duniya yawan mutane masu dauke da kwayar halittar cuta ta HIV.

XS
SM
MD
LG