Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Dab Da Ceto Ma'aikatan Hakar Kwal Da Suka Makale Cikin Rami Tun Ranar Laraba - 2002-07-28


Ma'aikatan agaji a yankin kudu maso yammacin Jihar Pennsylvania a nan Amurka, sun ce nan da 'yan sa'o'i kadan zasu kai ga ma'aikatan hakar kwal su tara, wadanda tun ranar laraba ruwa ya toshe su a krkashin kasa.

Kungiyoyin agajin sun bantare fallen dutse guda daya da ya rage a wani ramin da suka tona musamman domin zakulo mutanen daga cikin rami mai dan karen sanyin da mutanen ke ciki.

Masu aikin agajin sun tone ramin a hankali domin kada su huda ta inda mutanen suke tsaye, iskar da suke shaka ta tsiyaye.

Jami'ai ba su san halin da mahakan suke ciki ba a yanzu.

Wadannan mahaka suna tonon kwal ne a yankin kudu maso yammacin jihar Pennsylvania, sai suka yi kuskuren huda wani tsohon ramin hakar kwal dake cike da ruwa, abinda ya haddasa ambaliyar lita fiye da miliyan 200 na ruwa zuwa cikin ramin da mahakan suke.

XS
SM
MD
LG