Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 12 Sun Hallaka A Tashin Hankali Yau Lahadi A Isra'ila - 2002-08-04


Wani harin kunar bakin wake da aka kai kan wata motar safa a arewacin Isra'ila, da kuma wani hari na bindiga a birnin Qudus sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 12. 'Yan Isra'ila da dama sun ji rauni a wannan tashin hankali na baya-bayan nan, inda dukkan Falasdinawan da suka kai harin su ma suka mutu.

Dakarun tsaron Isra'ila sun bindige suka kashe wani Bafalasdine a lokacin mummunar musanyar wuta a kusa da Kofar Damascus, daya daga cikin kofofin shiga cikin birnin Qudus na asali.

Wannan Bafalasdine ya bude wuta haka kwatsam, ya haddasa mummunar musanyar wuta inda wani jami'in tsaron Isra'ila da wani balarabe su8 ma suka rasa rayukansu.

Wannan harin ya biyo bayan na kunar bakin wake da aka kai kan wata motar safa dake cike da ma'aikata da sojoji a kusa da birnin Safed a arewacin Isra'ola. Wannan fashewa mai tsananin karfe ta yaye rufin motar, ta kuma maida ta tamkar murhun girki.

Kungiyar 'yan kishin Falasdinu ta Hamas ta dauki alhakin kai wannan harin. Ta bayyana harin a zaman na nuna jarumtaka domin daukar fansar shugaban sojan kungiyar, Salah Shehada, wanda Isra'ila ta kashe a wani harin makami mai linzami kan gidansa dake zirin Gaza. Isra'ila ta kashe yara kanana guda tara a wannan harin.

Kakakin kungiyar Hamas, Mahmoud Zahar, ya ce ya kamata a yanzu dukkan 'yan Isra'ila su dauki kansu tamkar abin kaiwa hari. Ya ce, "...a yanzu kowane dan Isra'ila ya zamo abinda zamu iya kaiwa hari, tun da Isra'ila tana amfani da kowane Bafalasdine a zaman abin kai wa hari."

Hamas ta ki bayyana sunan dan harin kunar bakin waken da ya far wa motar safar domin ta kare iyalansa daga daukar fansar Isra'ila.

XS
SM
MD
LG