Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Zata Binciki Harin Da Aka Kai A Wani Sansanin 'Yan Hijira A Uganda - 2002-08-06


Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce zata tura masu bincike zuwa yankin arewacin kasar Uganda, domin nemo dubban mutanen da suka gudu a sanadin harin da 'yan tawaye suka kai a kan sansanin 'yan hijirar jiya litinin.

Hukumar ta ce dukkan 'yan gudun hijirar su dubu 24 'yan kasar Sudan sun arce, a bayan da 'yan tawayen kungiyar "Lord's Resistance Army" suka kai hari kan wannan sansani.

Hukumar ta ce 'yan tawaye sun kashe mutane akalla 14 a wannan harin, yayin da a bisa dukkan alamu sun sace mutane 4 suka yi gaba da su.

A cewar hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta MDD, 'yan tawaye sun sace abinci da magunguna na kimanin dala dubu 150, suka kona motoci biyar, suka kuma lalata kayan aiki na ofis.

XS
SM
MD
LG