Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Sun Amince Da Shirin Tsagaita Bude Wutar Da Isra'ila Ta Gabatar - 2002-08-07


Majalisar mulkin kai ta Falasdinawa ta amince bisa manufa da wani shirin Bani Isra'ila wanda ya tanadi janye sojojinta sannu kan hankali daga yankunan da ta sake mamayewa kwanakin baya, yayin da su kuma Falasdinawa zasu kara karfafa matakan tsaro.

A yau laraba shugaban Falasdinawa Yasser Arafat ya jagoranci taron majalisar zartaswarsa a birnin Ramallah inda suka tattauna wannan tayi na Isra'ila.

A bayan taron, ministan tsare-tsaren Falasdinawa, Nabil Shaath, ya ce majalisar ta bada amincewar farko ga wannan shiri na Isra'ila. Amma kuma ya ce akwai bukatar sake tattauna wasu bangarorin wannan shiri.

Ministan tsaron Bani Isra'ila, Binyamin Ben-Eliezer, shine ya gabatar da wannan tayi ranar litinin.

XS
SM
MD
LG