Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Shugaban Kenya Da Kada Ya Nada Magajinsa - 2002-08-07


Manyan 'ya'yan jam'iyyar KANU mai mulkin kasar Kenya, suna kokarin hana shugaba Daniel Arap Moi zaben mutumin da zai yi wa jam'iyyar takarar kujerar shugaban kasa a watan Disamba.

Jaridar "Daily Nation" ta Kenya ta ce mataimakin shugaban jam'iyyar, George Saitoti, da babban sakatarenta, Raila Odinga, da tsohon shugaban jam'iyyar, Joseph Kamotho, sun kulla kawance domin su yi kokarin tabbatar da cewa an gudanar da zaben dimokuradiyya wajen fitar da dan takara.

Shugaba Moi ya ce ya fi kaunar ganin Uhuru Kenyatta ya zamo shugaban kasar na gaba. Mr. Uhuru Kenyatta dai da ne na tsohon shugaban Kenya, Jomo Kenyatta, shugaban kasar na farko, kuma mutumin da Mr. Moi ya gada.

A bayan Mr. Kenyatta, shi ma kansa Mr. Odinga yana son jam'iyyar ta tsayar da shi takarar shugaban kasa. Sauran wadanda ke neman wannan matsayi sun hada da ministan sufuri, Musalia Mudavadi, da ministan yada labarai da bunkasa yawon shakatawa Kalonzo Musyoka, da kuma ministan kasa Katana Ngala.

XS
SM
MD
LG