Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar Ta Kwato Barikin Soja Daga Masu Bore - 2002-08-07


Jami'an Nijar sun ce sojojin gwamnati sun kwato wani barikin soja wanda sojoji masu bore dake neman karin albashi suka kwace.

Sojojin Nijar sun kai farmaki kan wannan barikin sojoji dake garin N'Guigmi, inda sojoji masu tawayen suka nemi mafaka a bayan da dakarun gwamnati suka fatattake su daga garin Diffa a kudu maso gabashin kasar.

A bayan da aka kwato garin na N'Guigmi daga hannun 'yan tawaye, ministan tsaron Nijar, Sabiou Dadi Gao, ya ce an kama masu tawaye da dama. Har ila yau an sako mutanen da suka kama suka yi garkuwa da su.

Sojojin sun fara yin tawaye kimanin mako guda da ya shige, a lokacin da suka kama garin Diffa suka sace jami'an gwamnati da dama.

Jami'ai sun yi tattaki har zuwa garin na N'Guigmi domin su tattauna da masu boren. Amma ministan tsaro Sabiou Gao ya ce tattaunawa ta wargaje a bayan da 'yan tawayen suka bukaci lallai da a ba su tabbacin cewa ba za a kore su daga aikin soja ba idan aka kawo karshen wannan rikici.

A ranar litinin wasu sojojin masu tawaye suka yi kokarin abkawa cikin rumbunan tara makamai guda uku a Niamey, babban birnin kasar. Sojojin gwamnati suka ce sun murkushe wannan tawaye a bayan da aka yi sa'o'i da dama ana musanyar wuta.

Kwana guda bayan wannan, shugaba Mamadou Tandja ya roki sojojin masu bore da su koma bakin aikinsu ba tare da jinkiri ba. Har ila yau ya lashi takobin cewa gwamnati zata hukumta wadanda suka haddasa wannan bore.

XS
SM
MD
LG