Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudi Arabiya Ta Ce Sam Ba Zata Kyale Amurka Ta Kai Hari Kan Iraqi daga Wani Yankin Kasarta Ba - 2002-08-07


Saudi Arabiya ta ce ta bayyanawa Amurka a fili cewar ba zata kyale sojojin Amurka su kai hari kan Iraqi daga wani yankin kasar Sa'udiyya ba.

A cikin hirar da yayi da kamfanin dillancin labaran "Associated Press" ministan harkokin wajen Sa'udiyya, Yarima Sa'ud al-Faisal, ya ce kasar tana yin adawa da duk wani matakin kai harin ad Amurka zata dauka a kan Iraqi, a saboda ta yi imani da cewa Iraqi tana kokarin sake kyale sufetocin Majalisar Dinkin Duniya su koma kasar domin binciken makaman kare dangi.

Ministan harkokin wajen ya ce gwamnatin sa'udiyya ba ta yin adawa da matakan sojan da Amurka talke dauka na kula da sararin samaniyar Iraqi daga wata cibiyar kula da zirga-zirgar abubuwa a sama dake Sa'udiyya. Amma kuma ya ce dole ne duk wani sauyin gwamnati a kasar Iraqi ya zamo daga su al'ummar Iraqin.

XS
SM
MD
LG