Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 14 Sun Mutu A Harbe-Harbe Kusa Da Birnin Kabul - 2002-08-07


Mutane su akalla 14 sun mutu, a bayan da wasu 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka kai hari kan wani caji ofis na 'yan sanda a kusa da Kabul, babban birnin Afghanistan.

Jami'an Afghanistan sun fada larabar nan cewar 'yan bindigar Larabawa ne da 'yan Pakistan, kuma an ga alamun cewa kungiyar al-Qa'ida ce ta kitsa wannan harin.

'Yan sanda suka ce an kashe 'yan bindiga akalla 11 da jami'an 'yan sanda biyu a dauki-ba-dadin da aka yi sa'o'i ana yi da bindigogi.

Wani farar hula da aka rutsa da shi a wannan fadan ma ya mutu.

Wannan fada wanda shine mafi muni da aka gani cikin wata da watanni a kusa da babban birnin na Afghanistan, ya zo kwana guda a bayan da sojojin Amurka dake sintiri a gabashin kasar suka harbe suka kashe 'yan afghanistan hudu da suka bude musu wuta. An raunata sojan Amurka guda daya.

XS
SM
MD
LG