Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taiwan Ta Ce Ba Zata Jefa Kuri'ar Raba-Gardama Ba, Sai Idan An Tilasta Mata - 2002-08-08


Taiwan ta ce ba zata gudanar da kuri'ar raba-gardama a kan batun 'yanci ba, sai fa idan tura ta kai bango daga hukumomin China.

Ma'aikatar kula da harkokin da suka shafi hulda da China babba, ta fada cikin wata takardar manufar da ta fito da ita yau alhamis cewa gwamnati tana zana dokar gudanar da kuri'ar raba-gardama, amma ba zata yi aiki da ita ba sai fa idan hukumomin birnin Beijing sun tilastawa tsibirin sake hadewa da China babba karkashin manufar nan ta kasa daya mai bin tafarki biyu.

A ranar asabar da ta shige, shugaba Chen Shui-Bian na Taiwan yayi kiran da a gudanar da kuri'ar raba-gardama domin yanke shawara kan makomar tsibirin, ya kuma bayyana China da Taiwan a zaman kasashe dabam-dabam guda biyu.

Wannan furuci nasa ya harzuka China wadda take daukar Taiwan a zaman lardinta dake son bijirewa.

XS
SM
MD
LG