Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 400 Suka Mutu A Madagascar A Saboda Cutar Mura - 2002-08-13


Jami'an lafiya sun ce yawan mutanen da suka mutu daga annobar cutar murar nan mai tsanani da ake kira "FLU" a turance ya kai kimanin 400 a kasar Madagascar.

Wasu mutanen su fiye da dubu 5 sun kamu da kwayar cutar dake haddasa irin wannan mura, wadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana a zaman kwayar cutar Flu nau'in "A."

A cikin makon nan ake sa ran wata tawagar kwararru ta hukumar lafiya zata isa Madagascar domin taimakawa gwamnati wajen yakar wannan mummunar annoba.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce dalilin da ya sa annobar murar tayi tsanani a Madagascar shine kasar matalauciya ce, kuma ba ta da wadatattun asibitoci, musamman a yankunan karkara. Har ila yau, hukumar ta ce wannan nau'in kwayar cuta sabuwa ce a kasar, a saboda haka jikin mutanen kasar bai gina kariya daga wannan cuta ba.

XS
SM
MD
LG