Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Umurci Mutane Dubu Hamsin Su Bar Gidajensu A Birnin Prague - 2002-08-13


Hukumomi a birnin Prague sun bada umurnin kwashe mutane har dubu hamsin daga gidajensu, a yayin da ambaliyar ruwa mafi muni da aka taba gani cikin shekaru masu yawan gaske, take yin barazana ga babban birnin na Jamhuriyar Czech.

Kwana da kwanakin da aka yi ana juye ruwan sama kamar da bakin kwarya, ya sa kogin Vlatava da ya bi ta cikin wannan birni ya cika ya batse. Masana yanayi sun yi hasashen cewa ana shirin fuskantar karin ruwan sama.

An kafa dokar-ta-baci a wasu larduna da dama na kasar ta Czech.

Har ila yau, an juye ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu kasashen makwabtan jamhuriyar Czech, kamar Jamus da kasar Austriya, inda aka ayyana birnin Salzburg a zaman yankin dake fuskantar bala'i.

A cikin mako gudan da ya shige, ruwan sama kamar da bakin kwarya a fadin nahiyar turai ya haddasa ambaliyar da aka jima ba a ga mai muninta ba, inda har mutane fiye da 70 suka mutu.

XS
SM
MD
LG