Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Da Ta Kudu Sun Cimma Daidaituwa - 2002-08-13


Koriya ta Arewa da ta Kudu sun kammala rana ta biyu ta tattaunawar manyan jami'ansu a birnin Seoul, inda kowane bangare yake bada rahoton samun ci gaba a kan wasu muhimman batutuwan da suke rikici kai.

Kamfanin dillancin labaran Koriya ta Kudu ya ce mashawarta suna rubuta sanarwar hadin guiwa a kan yarjejeniyoyi fiye da 12 da ake sa ran za a cimma, a wurin wannan taron kwana uku da za a kammala gobe laraba.

Jami'ai suka ce tattaunawar da ake yi tana mayar da hankali kan hanyoyin aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a wurin wani taron kolin da sassan suka yi a watan Yunin 2000. Yarjejeniyoyin sun hada da sake hada iyalai da 'yan'uwan da suka rabu da juna a sanadin yakin Koriya, da fadada hadin kan tattalin arziki da na soja, da kuma sake hada layin dogon da aka katse kafin barkewar yakin Koriya a 1950.

XS
SM
MD
LG