Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Sashen Hausa Na Muryar Amurka - 2002-08-13


Sunday Dare shine shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, kuma tun kafin zuwansa nan Muryar Amurka a shekarar 2001, sanannen dan jarida ne a ciki da wajen Nijeriya. A shekarar 1998 Mr. Dare ya samu gurbin karo ilmin aikin jarida a Jami'ar New York, ya kuma sake samun irin wannan gurbi zuwa Jami'ar Harvard dake Cambridge a Jihar Massachussetts a shekarar 2000. Babban aikin da ya sanya a gaba yanzu shine kokarin tabbatar da cewa an biya wa masu sauraronmu bukatunsu na maido da shirye-shiryen dare a ranakun asabar da lahadi.

Donnie Butler ita ce Fardusa, ko kuma jami'ar dake kula, tare da bada umurni wajen harhada shirye-shirye. Donnie ta jima tana aiki a nan Sashen Hausa na Muryar Amurka, akwai ta kuma da kwazon aiki. Har ma mu a nan Sashen Hausa muna kiranta "agogon sarauniyar aiki." Donnie Butler tana kaunar Hausa da Hausawa, da kuma abincin Hausawa, musamman ma tuwon shinkafa da miyar taushe, ko kuma shinkafa dafa-duka.

Ibrahim Alfa Ahmed "Mai Kahon Karo" shine editanmu na duniyar gizo. A bayan wannan ma, yana shiryawa tare da gabatar da filin nan na "A Bari Ya Huce..." da kuma shirin "Ra'ayoyin Masu Sauraro" a kowane mako. Kafin ya taho nan Sashen Hausa a shekarar 1991, Ibrahim yayi aiki a NTA Bauchi. Kuma shi masoyin na'urori ne masu kwakwalwa, da wasanni, da kuma wake-wake da kade-kaden gargajiya da na zamani.

Jummai Ali Maiduguri Edita ce, kuma ita ce ke gabatar da shirin nan na "Lafiya Uwar Jiki" inda ake amsa tambayoyin masu sauraro game da batutuwan da suka shafi lafiya. Jummai ta fara aiki a Muryar Amurka tun shekarar 1984. Kafin nan kuwa, Jummai ta yi shekaru da dama tana aikin jarida a Kaduna.

Aliyu Mustapha Sokoto, "Gadanga Dokin Karfe" shi ma edita ne, kuma shine jagoran shirye-shiryen nan na "Amsoshin Tambayoyinku" da "Labarin Wasanni" wadanda kuke ji a ranakun asabar da lahadi. Aliyu yayi aiki a NTA Sokoto kafin ya taho nan Muryar Amurka a shekarar 1989. Aliyu ya jagoranci kungiyar nan ta "Zumunta" ta 'yan arewacin Nijeriya dake Amurka na tsawon shekaru da yawa dag kafa ta. A kwanakin baya kuma Allah Ya ba shi karuwa ta magaji, wanda aka radawa suna Usman. Allah Ya raya shi, amin.

Hadiza Isa Wada edita ce, kuma kwararriyar 'yar jarida. Ta taho nan Sashen Hausa na Muryar Amurka kai tsaye daga Jami'ar Kansas a inda tayi karatun babban digiri kan aikin jarida. Hadiza ita ce ke shiryawa da gabatar da shirye-shiryen nan na "Domin Iyali" da "Kimiyya da Fasaha" a ranakun talata da alhamis. Hadiza ta kuma taba yin aikin jarida a NTA Jos.

Alhaji Kabiru Fagge ya taho sashen Hausa na Muryar Amurka daga gidan telebijin na NTA Kano. Kafin nan kuwa yayi aiki a kamfanin buga jaridun New Nigerian da kuma hukumar alhazai ta Nijeriya. Alhaji Kabiru Fagge edita ne a Sashen Hausa, kuma shine ke jagorancin shirin "Ilmi Garkuwar Dan Adam" da "Sharhin Jaridun Amurka" a ko wane mako.

Ahmed Yerima Dan mutanen Misau, yayi aiki a kafofin yada labarai da dama kafin ya iso nan Muryar Amurka. Yayi a gidan rediyon BRC na Bauchi, da Rediyo Moscow a kasar Rasha da kuma gidan rediyon BBC London. Gogan naku shine jagoran filin "Addini A Amurka" da kuma na "Sakonmu Na Mako". A bayan wasu harsunan na Nijeriya da gabashin Turai, Ahmed yana jin harshen Rashanci sosai.

Kabir Isa Jikamshi shine jami'in shirin "Mu Kewaya Duniya Mu Sha Labari", kuma shi ma dai masoyin wasanni ne da ayyukan motsa jiki. Kabir Isa na Jikamshi yayi aiki a gidan rediyon Muryar Jama'ar Jamus, Deutsche-Welle, da kuma NTA Bauchi kafin ya taho nan Muryar Amurka. Kabir yana kuma taya Gadanga wajen gabatar da filin "Amsoshin Tambayoyinku".

Halima Djimrao-Kane ta taho Sashen Hausa na Muryar Amurka daga gidan rediyon Anfani a Yamai, Jamhuriyar Nijar. Ita ce ke gabatar da shirye-shiryen "Noma Tushen Arziki" da "Hira da Baki", sannan tana tallafawa "mai Kahon karo" wajen gabatar da filin A Bari Ya Huce....Halima 'yar Jamhuriyar nijar ce, koda yake tayi karatun turancin Ingilishi a Jami'ar Obafemi Awolowo dake Ife a Nijeriya.

Aliyu Danladi Jibrin shine ke tallafawa Donnie Butler wajen bada umurni a dakinmu na watsa shirye-shirye, watau shine mataimakin Fardusanmu. Shine kuma babban jami'in dake kula da dukkan wasikun masu sauraronmu. Kafin zuwansa nan Amurka domin karatu a Jami'ar Strayer, Aliyu Danladi Jibrin, yayi aiki da FRCN Kaduna, a sashen kudi! Kwanakin baya Allah Yayi masa karuwa, lokacin da mai dakinsa ta haifi tagwaye, A'isha da Sa'a. Allah ya raya mana su.

XS
SM
MD
LG