Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyalan Wadanda Suka Mutu Ranar 11 Ga Watan Satumba Sun Kai Kara Kotu - 2002-08-15


Iyalan mutanen da suka mutu a hare-haren ta'addanci na ranar 11 ga watan Satumba zasu shigar da kara gaban kotu suna neman diyyar dala miliyan sau miliyan daya daga hannun mutane, da gwamnatoci, da kuma kungiyoyin da suka yi zargin cewa sun goyi baya, ko kuma sun taimaka wajen shirya kai harin.

Masu magana da yawun mutane fiye da 500 dake da hannu sun ce makasudin shigar da karar shine hana kungiyoyin ta'adda da masu goyon bayansu irin kudaden da suke bukata domin shiryawa da kai hare-hare nan gaba.

Yau alhamis za a shigar da karar gaban kotun tarayya a nan Washington.

Wadanda za a shigar da kara tasu sun hada da 'yan gidan sarautar Saudi Arabiya da dama, da bankuna 7 masu rassa a kasashe dabam-dabam na duniya, da kungiyoyin agaji na Musulmi guda 8, da gwamnatin kasar Sudan, da kuma kamfanin kwangilar 'yan'uwan Osama bin Laden, mutumin da ake jin shine ya kitsa hare-haren.

Gwamnatin shugaba Bush dai ba ta ce uffan ba a game da wannan kara.

XS
SM
MD
LG