Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musharraf Ya Ce Al-Qa'ida Tana Sake Kunno Kai A Afghanistan - 2002-08-20


Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan ya ce da alamun kungiyar al-Qa'ida tana dab da sake kunno kai a Afghanistan, watanni goma a bayan da aka murkushe kungiyar ta 'yan ta'adda a farmakin sojan da Amurka tayi wa jagoranci.

Shugaban na Pakistan ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar kasawar da rundunar sojojin kawancen dake karkashin jagorancin Amurka, da kuma gwamnatin rikon kwarya ta Afghanistan suka yi wajen shimfida ikonsu a wajen Kabul, babban birnin kasar, ta ba da kungiyar ta Osama bin Laden sukunin farfadowa.

Ya ce 'ya'yan al-Qa'ida suna kai gwauro da mari a bakin iyakokin Afghanistan, watakila suna tsallakawa cikin Pakistan. Ya ce da alamun ita ma kungiyar Taleban, wadda ta bada mafaka ga al-Qa'ida, tana sake farfadowa.

XS
SM
MD
LG