Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Kawo Karshen Farmaki A Bethlehem - 2002-08-20


'Yan sandan Falasdinu sun sake bazuwa a titunan birnin Bethlehem, a karkashin wata yarjejeniyar tsaron da ta kawo karshen farmakin sojan Isra'ila a birnin na yankin Yammacin kogin Jordan.

Sojojin Isra'ila sun ci gaba da yin sintiri a wajen birnin a yau, bayan da 'yan sandan Falasdinu suka fara shiga lokacin da sojojin Isra'ila suka janye da asubahin yau.

Har ila yau, Isra'ila ta ce zata janye sojojinta daga zirin Gaza idan har Falasdinawa zasu hana kai hare-hare a kan 'yan Isra'ila.

A halin da ake ciki, wani Bafalasdine dan kwanton-bauna daga kungiyar nan ta Hamas, ya harbe ya bindige wani sojan Isra'ila dake gadin wata unguwar share ka zauna ta Yahudawa a kudancin zirin Gaza.

Sojojin Isra'ila sun kashe wani saurayi Bafalasdine a wannan yanki, yayin da sojojin Isra'ila da suka kai farmaki cikin birnin Tulkarem a Yammacin kogin jordan suka kashe wani Bafalasdine dan bindiga.

XS
SM
MD
LG