Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Mamaye Ofishin Jakadancin Iraqi A Birnin Berlin - 2002-08-20


Wata kungiyar adawar Iraqi da ba a san da ita sosai ba, ta ce ta mamaye ofishin jakadancin Iraqi dake birnin Berlin, ta kuma bukaci shugaba Saddam Hussein da yayi murabus.

'Yan sandan Jamus, wadanda suka kewaye ginin ofishin, sun ce ana yin garkuwa da wasu mutane, cikinsu har da jakadan Iraqi a kasar Jamus.

Wannan kungiya dake kiran kanta "Kungiyar Adawar Iraqi Mai rajin Dimokuradiyya A Jamus", ta fada cikin wata sanarwar da ta bayar cewar ta kaddamar da gangamin lumana na wucin gadi domin jaddada kudurinta na ganin cewa an kawo karshen mulkin Saddam Hussein.

Kungiyar ta bayyana wannan mataki nata a zaman na farko a kokarin hambarar da shugaban na Iraqi.

'Yan sanda sun bada rahoton cewa mutane biyu sun ji rauni, amma ba su bada karin bayani ba. Jami'ai suka ce mutanen da kungiyar take yin garkuwa da su ba su kai goma ba.

Wasu makwabtan ofishin sun bada rahoton jin kararrakin harbe-harben bindiga, amma jami'ai sun kasa tabbatar da haka.

Babbar kungiyar adawar Iraqi mai hedkwata a London, "Iraqi National Congress" ta ce ba ta da alaka da kungiyar ta Berlin.

XS
SM
MD
LG