Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Da Kungiyoyin Kare Hakki Sun Yi Tur Da Hukumcin Kisa A Nijeriya... - 2002-08-20


Kungiyar Tarayyar Turai ta ce zata roki Nijeriya da kada ta aiwatar da hukumcin kisan da wata kotun Shari'ar Musulunci a Nijeriya ta yanke cewar a jefe wata macen da ta haihu ba tare da aure ba.

Wani kakakin Kungiyar tarayyar Turai ya ce kungiyarsu zata tado da wannan batu gaban hukumomin Nijeriya.

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa, ta ce tana rokon hukumomin Nijeriya da su yi wa matar ahuwa. Wani jami'in kasar Sweden ma ya bayyana damuwa kan wannan lamarin.

A jiya litinin, wata kotun Shari'ar Musulunci a Jihar Katsina dake arewacin Nijeriya, ta ki yarda da daukaka karar da Malama Amina Lawal mai shekaru 30 da haihuwa tayi, inda take neman da a soke hukumcin kisan da wata karamar kotu ta yanke cewar a jefe ta bayan da aka same ta da laifin yin zina. A karkashin dokar addinin Musulunci, a kan yanke hukumcin kisa kan mutumin da ya taba yin aure aka kuma same shi da laifin yin zina.

Su ma kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun yi tur da wannan hukumcin. Kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Human Rights Watch" mai hedkwata a New York, ta ce wannan "muguwar hanya ce ta ba ta dace ba ta yin aiki da Shari'ar Musulunci."

Kungiyar "Amnesty International" ta bayyana hukumcin da cewa "hanya mafi muni ce ta ganawa mutum azaba" wanda kuma ya sabawa tsarin mulkin Nijeriya.

XS
SM
MD
LG