Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ayyana Dokar-Ta-Baci Saboda Ambaliyar Ruwa A Wani Lardin China - 2002-08-21


Hukumomin China sun ayyana dokar-ta-baci saboda fargabar ambaliya a lardin Hunan dake kudancin kasar, inda miliyoyin mutane ke fuskantar barazana daga wani tabkin dake kara cika da ruwan sama.

An ce an tattara dubban ma'aikata domin su kara karfafa shingayen ruwa a kewayen makeken tabkin nan na Dongting, wanda tuni ya zarce matsayin ambaliya da mita daya da rabi.

Jami'ai suka ce suna tsammanin ruwan tabkin zai ci gaba da karuwa a yayin da kogunan dake kara cika da ruwan sama suke ci gaba da kwarara zuwa cikin wannan tabki wanda shine na biyu wajen girma daga cikin tabkunan dake samar da ruwan sha a kasar China.

Duka-duka, kafofin labaran kasar sun ce mutane miliyan goma, da kuma kadada dubu 667 na gonaki suna fuskantar barazana daga wannan tabki, wanda ke zaman wurin kwararar ruwan kogin Yangtze mai yawan yin ambaliya.

XS
SM
MD
LG