Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Kwamandan Sojojin Rwanda Ya Ki Amsa Laifin Kisan Kare-Dangi - 2002-08-21


Wani tsohon kwamandan sojojin kasar Rwanda, ya ki amsa laifin kashe-kashen kare-dangi a gaban wata kotun Majalisar Dinkin Duniya, MDD.

A yau laraba Janar Augustin Bizimungu ya bayyana gaban kotun dake bin kadin laifuffukan yaki a Rwanda, wadda take yin zama a birnin Arushar Tanzaniya. An tuhume shi da laifuffuka goma na kashe-kashen kare-dangi, hada baki domin aikata kashe-kashen kare-dangi, da kuma laifuffukan cin zarafin Bil Adama dangane da kisan kiyashin da aka yi wa jama'a a Rwanda a shekarar 1994.

janar Bizimungu, wanda aka kama cikin makon da ya shige a wani sansanin kwance damarar yakin 'yan tawayen UNITA a kasar Angola, yana daya daga cikin mutane 8 da aka fi nema ruwa a jallo, wadanda kuma aka tuhume su a gaban wannan kotu.

Ana zargin cewa yana daga cikin manyan mutanen da suka kitsa matakin da sojojin Rwanda da 'yan tsageran kabilar Hutu suka dauka na kashe mutane har dubu 800 'yan kabilar Tutsi da 'yan kabilar Hutu masu sassaucin ra'ayi.

Gwamnatin Rwanda ta bukaci da a mika mata Janar Bizimungu domin ya fuskanci tuhumar kisan kare-dangi, amma kuma kotun ta ki, tana mai cewa Rwanda ba ta da kayayyakin da zata iya gudanar da irin wannan shari'a.

XS
SM
MD
LG