Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Kai Farmaki Cikin sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Khan Younis - 2002-08-21


Sojojin Isra'ila sun kai farmaki cikin wani sansanin 'yan gudun hijira a zirin Gaza domin rushe gine-ginen da rundunar sojojin Bani Isra'ila ta ce Falasdinawa suna yin amfani da su wajen yin harbe-harbe a kan unguwannin share-ka-zauna na yahudawa dake kusa da nan.

An kashe wani Bafalasdine guda cikin wani ginin da ya rushe kansa a lokacin wannan farmaki na Isra'ila a Khan Younis.

Wannan farmaki ya zo kwana guda a bayan da wani Bafalasdine dan kwanton-bauna ya kashe wani sojan Isra'ila dake gadin wata unguwar yahudawa a yankin.

Jiya talata da maraice kuma, sojojin Isra'ila sun bindige suka kashe dan'uwan wani jigon 'yan kishin Falasdinu a birnin Ramallah dake yankin Yammacin kogin Jordan.

Rundunar sojojin Isra'ila ta ce an kashe Mohammad Saadat a lokacin da yayi kokarin tserewa.

XS
SM
MD
LG