Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Mai Bai Wa Shugaba Obasanjo Shawara Tayi Tur Da Hukumcin Kotun Shari'ar Musulunci - 2002-08-21


Wata mai bai wa shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya shawara ta soki hukumcin da wata kotun Shari'ar Musulunci ta yanke cewar a jefe wata mace har lahira saboda laifin zina.

Mai bai wa shugaba Obasanjo shawara kan harkokin mata, Titi Ajanaku, ta ce yadda ake aiwatar da Shari'ar Musulunci yana nuna wariya ga mata, yana kuma hukumta su game da lamarin da mutane biyu ne ke aikatawa.

Amma kuma a Jamhuriyar Nijar makwabciyar Nijeriya, kungiyar Musulmi mafi girma ta kasar ta ce wannan hukumcin da aka yanke kan Amina Lawal yayi daidai domin kare da'a, da kuma hana sauran mata yin zina a nan gaba.

A karkashin Shari'ar Musulunci, ana yanke hukumcin kisa kan macen da ta taba yin aure ta kuma aikata zina.

A ranar litinin kotun ta ki yarda da daukaka karar da Malama Amina tayi, ta ce za a zartas da wannan hukumci na jefewa da zarar ta yaye 'yarta. A cikin watan Maris aka fara samunta da laifi.

Wannan hukumci ya janyo suka daga kungiyoyin mata, da kungiyoyin kare hakkin bil Adama na duniya, da kuma kasashen waje, cikinsu har da Amurka, da Faransa da kuma Sweden.

Tarayyar Turai ta ce zata gabatar da takardar neman jami'an Nijeriya da kada su zartas da wannan hukumci.

XS
SM
MD
LG