Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Shugaba Obasanjo Yayi Tur Da Yunkurin Tsige Shugaban Na Nijeriya - 2002-08-21


Wata sanarwa daga ofishin shugaba Olusegun Obasanjon Nijeriya, ta bayyana barazanar da ake yi ta tsige shi tun daga makon da ya shige a zaman wata "abar nuna kyashi."

Sanarwar da aka bayar a yau laraba ta bayyana 'yan majalisar wakilan dake neman tsige shugaban da cewa masu nuna son kai ne kawai.

Musamman ma dai, sanarwar ta ce kuri'ar da aka jefa kan batun tsige shugaban, ta "nuna kyashi, da tsageranci ne, wadda ta sabawa tsarin mulkin Nijeriya, wadda aka kuma ake yin fatali da ita."

A makon da ya shige, majalisar wakilai tayi kira ga shugaba Obasanjo da yayi murabus cikin makonni biyu, ko kuma a tsige shi. Majalisar ta zarge shi da laifin zarmiya, da rashin mutunta doka tare da kin aiwatar da kasafin kudin da majalisa ta amince da shi.

A daidai lokacin da majalisar wakilan ta dauki wannan mataki ne sai shugaba Obasanjo ya bada umurnin da a binciki wasu muhimman ofisoshin gwamnati a bangaren majalisa da na shugaba da kuma na shari'a. Amma kuma ala tilas shugaban ya janye wannan umurni nasa bayan kwanaki uku, a lokacin da masu sukar lamiri suka ce yayi hakan ne domin dauke hankali daga wannan batu na tsige shi.

XS
SM
MD
LG