Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Australiya Ta Bi Sahun Masu Kokawa Da Hukumcin Kotun Shari'ar Musulunci A Nijeriya - 2002-08-22


Australiya ta bi sahun kasashen duniya dake nuna adawarsu da hukumcin da aka yanke kan wata mace a Nijeriya, wadda aka samu da laifin yin zina.

Ministan harkokin wajen Australiya, Alexander Downer, ya fada yau alhamis cewar kasarsa zata nuna tsananin fusata idan har aka zartas da hukumcin jefewa kan Amina Lawal mai shekaru 31 da haihuwa.

A ranar litinin wata kotun daukaka kara ta Shari'ar Musulunci a Jihar Katsina dake arewacin Nijeriya, ta ki yarda da daukaka karar da ta yi kan wannan hukumcin kisa, tana mai cewa za a aiwatar da wannan hukumci kamar yadda aka yanke tun farko.

wata mai bai wa shugaba Obasanjo na Nijeriya shawara kan harkokin mata, Titi Ajanaku, ita ma ta soki lamirin wannan hukumci. Wadanda suke bin sahunta wajen sukar wannan hukumci sun hada da kungiyoyin mata, da kungiyoyin kare hakkin bil Adama na kasa da kasa, da kasashe da dama cikinsu har da Amurka da Faransa da Sweden.

Sai dai kuma, kungiyar Musulmi mafi girma a Jamhuriyar Nijar makwabciyar Nijeriya, ta ce wannan hukumci da aka yankewa Amina Lawal yayi daidai domin hhana fasikanci a tsakanin jama'a tare da hana mata yin zina a nan gaba.

XS
SM
MD
LG