Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Abu Nidal Ce Ta Kai Harin Bam Na Lockerbie... - 2002-08-23


Wani tsohon mukarrabin Abu Nidal ya ce madugun 'yan ta'addar na Falasdinawa da aka bada rahoton mutuwarsa a makon da ya shige, ya fada masa cewar kungiyarsu ta "Fatah Revolutionary Council" ita ce ta kai harin bam na Lockerbie a shekarar 1988.

Atef Abubakar ya ce Abu Nidal shi da kansa ya bayyana wannan a lokacin wani taron manyan mukarrabansa, ya kuma yi barazanar kashe duk wanda ya fallasa wannan labarin. Za a buga furucin nasa yau Jumma'a a cikin jaridar nan ta Larabci mai suna "al-Hayat" da ake bugawa a London.

A shekarar da ta shige aka yanke hukumcin daurin rai da rai a gidan kurkuku a kan wani jami'in leken asiri na Libya dangane da harin bam din da ya kashe mutane 270 cikin jirgin saman kamfanin Pan Am da ya tarwatse a samaniyar garin Lockerbie na kasar Scotland, kan hanyarsa ta zuwa New York.

XS
SM
MD
LG