Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kashe Falasdinawa Biyu Mahara A Gaza - 2002-08-23


Isra'ila ta fadawa Majalisar Mulkin Kai ta Falasdinawa cewar zata dakatar da janye sojojinta daga yankunan da ta sake mamayewa kwanakin baya, har sai jami'an tsaron Falasdinawa sun dauki matakan murkushe masu kaiwa ita Isra'ila hare-hare.

Wannan shine sakon da ya bayyana a ganawar da aka yi yau Jumma'a tsakanin kwamandan sojojin Isra'ila a yankin Yammacin Kogin Jordan da jami'an tsaron Falasdinawa.

Sojojin Isra'ila a zirin Gaza, sun kashe wasu Falasdinawa biyu dauke da makamai wadanda suka ce sun yi kokarin kutsawa cikin wata unguwar yahudawa 'yan kama-wuri-zauna.

Kungiyar 'yan Shuhada'u ta al-Aqsa tayi ikirarin kokarin kai harin.

Wannan lamari ya faru 'yan sa'o'i kadan a bayan da ministan harkokin cikin gida na Majalisar Mulkin Kan Falasdinawa ya kasa shawo kan kungiyoyin kishin Falasdinu da su dakatar da kai hare-hare domin Isra'ila ta janye sannu cikin hankali daga yankunan da ta sake mamayewa.

XS
SM
MD
LG